5 Nan fa, a ƙasar Mowab Musa bawan Ubangiji ya mutu, yadda Ubangiji ya faɗa. 6 Aka binne shi[b] a Mowab, a kwarin kusa da Bet-Feyor, amma har wa yau babu wanda ya san inda kabarinsa yake. 7 Musa yana da shekara ɗari da ashirin sa’ad da ya mutu, duk da haka idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuwa bai ragu ba. 8 Isra’ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab kwana talatin, sai da lokacin kuka, da na makoki suka ƙare.
9 To, Yoshuwa ɗan Nun ya cika da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya hannuwansa a kansa. Saboda haka Isra’ilawa suka saurare shi, suka kuma aikata abin da Ubangiji ya umarci Musa.
10 Tun daga nan ba a sāke yin wani annabi a Isra’ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska, 11 wanda kuma ya yi dukan waɗannan alamu banmamaki da al’ajaban da Ubangiji ya aike shi yă yi a Masar, da a kan Fir’auna, da a kan dukan shugabanninsa, da kuma a kan dukan ƙasarsa. 12 Gama babu wani wanda ya taɓa nuna iko mai ƙarfi, ko yă aikata ayyukan banrazana waɗanda Musa ya yi a gaban dukan Isra’ila.
<- Maimaitawar Shari’a 33