15 Ku duba, na sa a gabanku a yau, rai da wadata, mutuwa da kuma hallaka. 16 Gama na umarce ku a yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, don ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma dokokinsa, sa’an nan za ku rayu, ku kuma ƙaru, Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a ƙasar da kuke shiga don ci gādonta.
17 Amma in zukatanku suka kangare, ba su kuwa yi biyayya ba, in kuma aka rinjaye ku don ku rusuna ga waɗansu alloli ku yi musu bauta, 18 na furta muku yau cewa tabbatacce za a hallaka ku. Ba za ku zauna a ƙasar da kuke hayewa Urdun don ku shiga ku ci gādonta ba.
19 A wannan rana na kira bisa sama da ƙasa a matsayin shaidu a kanku, cewa na sa a gabanku rai da mutuwa, albarku da la’anoni. Yanzu sai ku zaɓi rai, saboda ku da ’ya’yanku ku rayu 20 don kuma ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku saurari muryarsa, ku kuma manne masa. Gama Ubangiji shi ranku, zai kuwa ba ku shekaru masu yawa a ƙasar da ya rantse zai ba wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.
<- Maimaitawar Shari’a 29Maimaitawar Shari’a 31 ->