1 Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Mowab,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom
suka zama sai ka ce toka.
2 Zan sa wuta a Mowab
da za tă ƙone kagarun Keriyot*Ko kuwa na biranenta
Mowab za tă gangara cikin hayaniya mai girma
cikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho.
3 Zan hallaka mai mulkinta
zan kuma kashe shugabanninta.”
4 Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Yahuda,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji
ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba,
domin allolin ƙarya sun ruɗe su,
allolin da kakanninsu suka bauta.
5 Zan sa wuta a Yahuda
da za tă ƙone kagarun Urushalima.”
Hukunci a kan Isra’ila
6 Ga abin da Ubangiji ya ce,
“Saboda zunubai uku na Isra’ila,
har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.
Don sun sayar da adalai waɗanda
suka kāsa biyan bashinsu.
Sun kuma sayar da matalauta
waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.
7 Sun tattake kawunan matalauta
kamar yadda suke taka laka
suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya.
Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda,
suna kuma ɓata sunana mai tsarki.
8 Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade
a kan tufafin da suka karɓe jingina.
A gidajen allolinsu
sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara.
9 “Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu,
ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul
kuma mai ƙarfi kamar itacen oak.
Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama,
da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.
10 Na fitar da ku daga ƙasar Masar,
na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada
don in ba ku ƙasar Amoriyawa.
11 “Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza
waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku.
Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?”
In ji Ubangiji.
12 “Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi
kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.
13 “Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku
kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi.
14 Masu gudu da sauri ba za su tsira ba,
masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba,
jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba.
15 ’Yan baka ba za su iya dāgewa ba,
masu saurin gudu ba za su tsira ba
mahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba.
16 Ko jarumawa mafi jaruntaka
za su gudu tsirara a ranan nan,”