Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
27
Bulus ya tafi Roma a jirgin ruwa
1 Sa’ad da aka yanke shawara cewa za mu tashi a jirgin ruwa zuwa Italiya, sai aka danƙa Bulus da waɗansu ’yan kurkuku a hannun wani jarumin mai suna Juliyos, wanda yake na Bataliyar Babban Sarki. 2 Muka shiga jirgin ruwa daga Andiramitiyum wanda yake shirin tashi zuwa tasoshin da suke bakin tekun lardin Asiya, sai muka kama tafiya. Aristarkus, mutumin Makidoniya daga Tessalonika, yana tare da mu.

3 Kashegari muka sauka a Sidon; Juliyos kuwa, cikin alheri ga Bulus, ya bar shi yă je wajen abokansa domin su biya masa bukatunsa. 4 Daga can kuma muka sāke kama tafiya muka zaga ta bayan tsibirin Saifurus saboda iska tana gāba da mu. 5 Sa’ad da muka ƙetare tekun da yake sassan gaɓar Silisiya da Famfiliya sai muka sauka a Mira ta Lisiya. 6 A can jarumin ya sami wani jirgin ruwan Alekzandariyan da za shi Italiya sai ya sa mu a ciki. 7 Tafiyar ta ɗauki kwanaki da yawa muna yi kaɗan-kaɗan da ƙyar muka iso kusa da gaɓar Kinidus. Da iskar ta hana mu ci gaba, sai muka bi ta bayan tsibirin Kirit ɗaura da Salmone. 8 Muka ci gaba a gefen gaɓar da ƙyar har muka iso wani wurin da ake kira Kyakkyawan Mafaka, kusa da garin Laseya.

9 An riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya kuwa ta riga ta zama da hatsari domin a lokacin Azumi*Wato, da Ibraniyanci Ranar Kafara ke nan (Yom Kippur) ya riga ta wuce. Saboda haka Bulus ya gargaɗe su, 10 ya ce, “Mutane, ina gani tafiyarmu za tă zama da masifa ta kuma kawo babbar hasara ga jirgin ruwan da kaya, da kuma ga rayukanmu ma.” 11 Amma jarumin, a maimakon ya saurari abin da Bulus ya ce, sai ya bi shawarar matuƙi da kuma mai jirgin ruwan. 12 Da yake tashar jirgin ruwan ba tă dace a ci damina a can ba, yawanci suka ba yanke shawara cewa mu ci gaba da tafiya, da bege za mu kai Funis mu ci damina a can. Wannan tashar jirgin ruwa ne a Kirit, tana fuskantar kudu maso yamma da kuma arewa maso yamma.

Hadari
13 Da iska ta fara busowa daga kudu a hankali, sai suka yi tsammani sun sami abin da suke nema; saboda haka suka janye ƙugiyar jirgin ruwa suka bi ta gefen tsibirin Kirit. 14 Ba a jima ba, sai ga wata guguwar iska mai ƙarfin da ake kira “’Yar arewa maso gabas,” ta buga daga tsibirin. 15 Iskar ta ci ƙarfin jirgin ruwan har ya kāsa fuskantar iskar; saboda haka muka sallamar mata tă yi ta tura mu. 16 Da muka bi ta bayan wani ɗan tsibirin da ake kira Kauda, da ƙyar muka jawo ɗan ƙaramin jirgin kusa da jirgin. 17 Da mutanen suka jawo shi cikin babban jirgin ruwan, sai suka sa igiyoyi ta ƙarƙashin jirgin ruwan kanta don su ɗaɗɗaura shi. Don gudun kada a fyaɗa mu da yashin gaɓar Sirtis, sai suka saukar da ƙugiyar jirgin ruwan, suka bari aka yi ta tura jirgin haka. 18 Haka muka yi ta shan bugun guguwar hadarin nan kashegari suka fara jajjefar da kayan da jirgin yake ɗauke da su a cikin teku. 19 A rana ta uku, da hannuwansu suka jefar da kayan aikin jirgin ruwan a cikin teku. 20 Da dai aka yi kwana da kwanaki ba a ga rana ko taurari ba guguwar iska kuma ta ci gaba da bugowa, a ƙarshe muka fid da zuciya za mu tsira.

21 Bayan mutanen sun daɗe ba su ci abinci ba, Bulus ya miƙe tsaye a gabansu ya ce, “Mutane, da kun ji shawarata na kada ku tashi daga Kirit, da ba ku fāɗa wannan masifa da hasara ba. 22 Amma yanzu ina ƙarfafa ku ku yi ƙarfin hali, domin ba ɗayanku da zai rasa ransa; jirgin ruwan ne kaɗai zai hallaka. 23 Jiya da dare wani mala’ikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni 24 ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lalle za ka tsaya a gaban Kaisar a yi maka shari’a; Allah kuma cikin alherinsa ya ba ka dukan rayukan mutanen da suke tafiya tare da kai.’ 25 Saboda haka ku yi ƙarfin hali, ku jama’a, gama gaskata Allah a kan cewa yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka zai faru. 26 Duk da haka, dole a fyaɗa mu a wani tsibiri.”

Jirgin ruwa ya yi hatsari
27 A dare na goma sha huɗu iska dai tana ta korarmu a Tekun Adiriyatik, wajen tsakar dare sai masu tuƙin jirgin suka zaci sun yi kusa da ƙasa. 28 Sai suka gwada zurfin ruwan suka ga ya kai ƙafa ɗari da ashirin. Bayan ɗan lokaci kaɗan suka sāke gwadawa suka ga zurfin ya kai ƙafa tasa’in. 29 Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki ƙugiyoyin jirgin guda huɗu daga bayan jirgin suka yi fata gari ya waye. 30 Cikin ƙoƙarin tserewa daga jirgin, sai masu tuƙin jirgin suka saukar da ɗan ƙaramin jirgin ruwan cikin tekun, suka yi kamar za su saki waɗansu ƙugiyoyi daga sashen gaba na babban jirgin ne. 31 Sai Bulus ya ce wa jarumin da kuma sojojin, “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba za ku tsira ba.” 32 Sai sojojin suka yayyanke igiyoyin da suke riƙe da ɗan ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.

33 Kafin gari ya waye Bulus ya roƙe su duka su ci abinci. Ya ce, “Kwana goma sha huɗu ke nan, kuna zama cikin zulumi kun kuma kasance ba abinci, ba ku ci kome ba. 34 Ina roƙonku yanzu ku ci abinci. Kuna bukatarsa don ku rayu. Ba ɗayanku da zai rasa ko gashin kansa guda ɗaya.” 35 Bayan da ya faɗi haka, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya ga Allah a gabansu duka. Sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci. 36 Dukansu kuwa suka sami ƙarfafawa, suka kuma ci abinci. 37 Dukanmu a jirgin kuwa mutane 276 ne. 38 Sa’ad da suka ci iyakar abin da suke so, sai suka rage nauyin jirgin ta wurin zubar da hatsin a cikin tekun.

39 Da gari ya waye, ba su gane ƙasar da suke ba, amma suka ga wani lungu da gaci mai yashi, sai suka yanke shawara su kai jirgin can in za su iya. 40 Da suka yanke ƙugiyoyin, sai suka bar su a cikin teku a lokaci guda kuma suka ɓalle maɗaurin abin juya jirgin. Sai suka tā da filafilan gaban jirgin daidai yadda iska za tă tura shi gaba, sa’an nan suka nufi gaci. 41 Amma jirgin ruwan ya shiga yashi ya kafe. Kan jirgin ya shiga cikin yashin ya kāsa motsi, sai jirgin ya fara farfashewa ta baya saboda haukan raƙuman ruwa.

42 Sojojin suka yi niyya su kakkashe ’yan kurkukun don hana waninsu yă yi iyo yă tsere. 43 Amma jarumin ya so yă ceci ran Bulus, sai ya hana su aiwatar da niyyarsu. Ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci. 44 Sauran kuma su bi katakai zuwa can ko kuma a kan tarkacen jirgin ruwan. Ta haka kowa ya kai bakin teku lafiya.

<- Ayyukan Manzanni 26Ayyukan Manzanni 28 ->