5 Amma Yahudawa suka yi kishi; saboda haka suka tattara ’yan iska daga kasuwa, suka shirya wata ƙungiya, suka tā da tarzoma a birni. Suka ruga zuwa gidan Yason suna neman Bulus da Sila don su kawo su a gaban taron. 6 Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ’yan’uwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa, “Waɗannan mutanen da suke tā da fitina ko’ina a duniya sun iso nan, 7 Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.” 8 Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi. 9 Sai suka sa Yason da sauran su biya kuɗin saki sa’an nan suka sallame su.
13 Da Yahudawan da suke a Tessalonika suka ji cewa Bulus yana wa’azin maganar Allah a Bereya, sai suka je can ma, suna zuga taro suna kuma tā da hankalinsu. 14 Nan da nan ’yan’uwa suka sa Bulus yă tafi bakin teku, amma Sila da Timoti suka dakata a Bereya. 15 Mutanen da suka raka Bulus kuwa suka kawo shi Atens sa’an nan suka dawo da umarnai wa Sila da Timoti cewa su zo wurinsa da gaggawa.
22 Sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyar taron Areyofagus ya ce, “Ya ku mutanen Atens! Na dai lura cewa ta kowace hanya ku masu addini ne ƙwarai. 23 Gama sa’ad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu,
24 “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. 25 Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. 26 Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. 27 Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. 28 ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’
29 “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa. 30 A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba. 31 Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.”
32 Sa’ad da suka ji maganar tashin matattu, waɗansunsu suka yi tsaki, amma waɗansu suka ce, “Muna so mu ƙara jin ka a kan wannan batu.” 33 Da wannan, Bulus ya bar Majalisar. 34 Waɗansu mutane kima suka zama mabiyan Bulus suka kuwa gaskata. A cikinsu kuwa akwai Diyonasiyus ɗan Majalisar Areyofagus, haka kuma wata mace mai suna Damaris, da waɗansu dai haka.
<- Ayyukan Manzanni 16Ayyukan Manzanni 18 ->