3 Yohanna
1 Dattijon nan,
5 Abokina ƙaunatacce, kana da aminci cikin abin da kake yi wa ’yan’uwa, ko da yake su baƙi ne a gare ka. 6 Sun faɗa wa ikkilisiya game da ƙaunarka. Za ka kyauta in ka sallame su a hanyar da ta cancanci Allah. 7 Saboda Sunan nan ne suka fito, ba sa karɓan wani taimako daga waɗanda ba masu bi ba. 8 Saboda haka ya kamata mu nuna halin karɓan baƙi ga irin mutanen nan domin mu yi aiki tare saboda gaskiyan nan.
9 Na rubuta wa ikkilisiya, amma Diyotirefes, wanda yake son zama na farko, ya ƙi yă yi hulɗa da mu. 10 Saboda haka in na zo, zan tone abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har yana ƙin marabtar ’yan’uwa. Yana hana waɗanda suke so yin haka, yana ma korinsu daga ikkilisiya.
11 Abokina ƙaunatacce, kada ka yi koyi da abin da yake mugu sai dai abin da yake nagari. Duk mai yin abin da yake nagari daga Allah yake. Duk mai yin abin da yake mugu bai taɓa sanin Allah ba. 12 Demetiriyus yana da shaida mai kyau daga wurin kowa, har gaskiya kanta ma ta shaide shi. Mu ma muna ba da shaida mai kyau a kansa, ka kuma san cewa shaidarmu gaskiya ce.