2 Bitrus
1 Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi,
5 Saboda haka, ku yi iyakar ƙoƙari ku ƙara wa bangaskiyarku nagarta; ga nagarta kuwa, ku ƙara mata sani; 6 ga sani kuma ku ƙara masa kamunkai; ga kamunkai kuma ku ƙara da daurewa; ga daurewa kuwa ku ƙara da tsoron Allah; 7 ga tsoron Allah kuma ku ƙara da nuna alheri ga ’yan’uwa; ga nuna alheri ga ’yan’uwa kuma ku ƙara da ƙauna. 8 Domin in kuna ƙaruwa a waɗannan halaye, za su kāre ku daga rashin tasiri da rayuwa na rashin amfani cikin saninku na Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9 Amma in wani ba shi da su, ba shi da hangen nesa ke nan kuma makaho ne, ya kuma manta cewa an tsarkake shi daga zunubansa na dā.
10 Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba, 11 za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.
16 Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo sa’ad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido. 17 Gama ya sami girma da ɗaukaka daga Allah Uba sa’ad da murya ta zo masa daga Mafificiyar Ɗaukaka cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; da shi nake jin daɗi ƙwarai.”[a] 18 Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama sa’ad da muke tare da shi a kan dutse mai tsarki.
19 Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku. 20 Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa. 21 Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.
2 Bitrus 2 ->- a Mat 17.5; Mar 9.7; Luk 9.35