Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
11
(1 Sarakuna 12.21-24)

1 Sa’ad da Rehobowam ya iso Urushalima, ya tattara mayaƙa dubu ɗari takwas daga gidan Yahuda da Benyamin, don su yi yaƙi da Isra’ila su sāke mai da mulki wa Rehobowam.

2 Amma wannan maganar Ubangiji ta zo ga Shemahiya mutumin Allah. 3 “Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon sarkin Yahuda da kuma dukan Isra’ilawan da suke a Yahuda da Benyamin, 4 ‘Ga abin da Ubangiji ya ce kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku. Ku tafi gida kowannenku, gama wannan yi na ne.’ ” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubangiji suka kuma koma daga takawa don yaƙi da Yerobowam.

Rehobowam ya gina katanga kewaye da Yahuda
5 Rehobowam ya zauna a Urushalima ya kuma gina garuruwa don kāriya a cikin Yahuda. 6 Betlehem, Etam, Tekowa, 7 Bet-Zur, Soko, Adullam, 8 Gat, Maresha, Zif, 9 Adorayim, Lakish, Azeka, 10 Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin. 11 Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi. 12 Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.

13 Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi. 14 Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da ’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji. 15 Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi. 16 Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu. 17 Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.

Iyalin Rehobowam
18 Rehobowam ya auri Mahalat, ’yar Yerimot ɗan Dawuda wadda Abihayil ’yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa. 19 Ta haifa masa ’ya’ya maza. Yewush, Shemariya da Zaham. 20 Sa’an nan ya auri Ma’aka ’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit. 21 Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka ’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da ’ya’ya maza ashirin da takwas da ’ya’ya mata sittin.

22 Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin ’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki. 23 Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu ’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa.

<- 2 Tarihi 102 Tarihi 12 ->