1 A ƙarshe, ’yan’uwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau. 2 Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu.
3 Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; 4 don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, 5 ba cikin muguwar sha’awa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; 6 cikin wannan al’amari kuwa kada wani yă yi wa ɗan’uwansa laifi ko yă cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. 7 Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki. 8 Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.
9 Yanzu kuwa game da ƙaunar ’yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna. 10 Gaskiyar kuwa ita ce, kuna ƙaunar dukan ’yan’uwa ko’ina a Makidoniya. Duk da haka muna ƙara gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku yi haka sau da sau. 11 Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga sha’anin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku, 12 don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.
Zuwan Ubangiji
13 ’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14 Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. 15 Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16 Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17 Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. 18 Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.
<- 1 Tessalonikawa 31 Tessalonikawa 5 ->