1 Duk sa’ad da Sama’ila ya yi magana dukan Isra’ila sukan saurare shi.
4 Saboda haka mutanen suka aika waɗansu maza zuwa Shilo, suka kuwa tafi suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Maɗaukaki wanda yake zaune tsakanin Kerubobi. ’Ya’yan Eli biyun nan Hofni da Finehas suna wurin tare da akwatin alkawarin Ubangiji.
5 Da aka shigo da akwatin alkawarin Ubangiji a cikin sansani, sai Isra’ilawa suka tā da babbar murya har ƙasa ta jijjiga. 6 Da jin wannan, Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, “Me ke kawo wannan ihu mai ƙarfi haka a sansanin Isra’ilawa?”
10 Saboda haka Filistiyawa suka yi yaƙi, Isra’ilawa kuwa suka sha ɗibga, kowane mutum kuwa ya gudu zuwa tentinsa. Kisan kuwa ya yi muni ƙwarai. Isra’ilawa sun rasa mayaƙa dubu talatin. 11 Aka ƙwace akwatin alkawarin Ubangiji. Aka kuma kashe ’ya’yan Eli biyu, Hofni da Finehas.
14 Eli ya ji ihun ya yi tambaya ya ce, mene ne dalilin wannan ihu?
16 Mutumin ya gaya wa Eli cewa, “Shigowata ke nan daga bakin dāgā. Na kuɓuce daga can yau ɗin nan.”
17 Mutumin da ya kawo labarin ya ce, “Isra’ilawa sun gudu a gaban Filistiyawa, mayaƙan kuma sun sha mummunar ɗibga. ’Ya’yanka Hofni da Finehas su ma sun mutu. Aka kuma ƙwace akwatin alkawarin Allah.”
18 Da ya ambaci akwatin alkawarin Allah, sai Eli ya fāɗi da baya daga kujeransa kusa da ƙofa, wuyarsa ta karye, ya kuma mutu domin ya tsufa ƙwarai. Ya yi shugabancin Isra’ila shekaru arba’in.
19 Matar Finehas, ɗansa tana da ciki a lokacin ta kuma kusa haihuwa. Sa’ad da ta ji labari cewa an ƙwace akwatin alkawarin Allah, ta kuma labarin surukinta da mijinta sun mutu, sai ta shiga naƙuda, ta kuma haihu. Amma naƙuda ta sha ƙarfinta. 20 Da tana mutuwa, matan da suke lura da ita suka ce, “Kada ki karaya kin haifi ɗa namiji.” Amma ba tă ba da amsa ko tă kula ba.
21 Ta ba wa yaron suna Ikabod, ma’ana “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila”, domin an ƙwace akwatin alkawarin Allah, domin kuma mutuwar surukinta da na mijinta. 22 Ta ce, “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila, gama an ƙwace akwatin alkawarin Allah.”
<- 1 Sama’ila 31 Sama’ila 5 ->- a Ebenezer wato, dutsen taimako