3 Daga can Dawuda ya tafi Mizfa a Mowab. Ya ce wa sarkin Mowab, “Za ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Allah zai yi da ni?” 4 Saboda haka ya bar su a wurin sarkin Mowab, suka zauna da shi duk tsawon lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu.
5 Amma annabin nan Gad ya ce wa Dawuda, “Kada ka zauna a nan, maza ka tashi ka shiga ƙasar Yahuda”. Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Heret.
9 Amma Doyeg mutumin Edom da yake tsaye tare da fadawan Shawulu ya ce, “Na ga ɗan Yesse ya zo wurin Ahimelek ɗan Ahitub a Nob. 10 Ahimelek ya roƙi Ubangiji saboda shi, ya kuma ba shi guzuri da takobin Goliyat Bafilistin.”
11 Sai sarki ya aika aka kira masa Ahimelek firist ɗan Ahitub da dukan iyalin mahaifinsa. Dukansu suka zo wurin sarki. 12 Shawulu ya ce, “Ka saurara yanzu, ɗan Ahitub.”
13 Shawulu ya ce masa, “Don me ka gama baki da ɗan Yesse a kaina har ka ba shi burodi da takobin (Goliyat), ka kuma roƙi Allah don yă tayar mini, yă kuma yi fakona kamar yadda yake yi yau?”
14 Ahimelek ya ce wa sarki, “A cikin bayinka duka, wa ke da aminci iri na Dawuda, surukin sarki, shugaban jarumanka wanda ake girmamawa da gaske a gidanka? 15 A wannan rana ce da na fara roƙon Allah saboda shi? Kada sarki yă zargi bawansa ko wani daga iyalin mahaifinsa, gama bawanka bai san kome a kan dukan waɗannan al’amura ba.”
16 Amma sarki ya ce, “Lalle Ahimelek za ka mutu, da kai da dukan iyalin mahaifinka.”
17 Sai sarki ya umarci matsaran da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Ku kakkashe firistocin Ubangiji, gama su ma sun goyi bayan Dawuda. Sun san yana gudu, duk da haka ba su gaya mini ba.”
18 Sai sarki ya umarce Doyeg ya ce, “Ka juya ka kakkashe firistocin.” Doyeg mutumin Edom ya juya ya kakkashe firistocin. A ranar kuwa ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke sanye da efod na lilin. 19 Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakuna, da kuma tumaki.
20 Amma Abiyatar ɗan Ahimelek jikan Ahitub ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda. 21 Abiyatar gaya wa Dawuda cewa, “Shawulu ya hallaka firistocin Ubangiji.” 22 Dawuda ya ce wa Abiyatar, “Lalle a wancan ranar, sa’ad da na ga Doyeg mutumin Edom a can, na san tabbatacce zai gaya wa sarki. Ni ne sanadin mutuwar dukan iyalin mahaifinka. 23 Ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro mutumin da yake neman ranka, yana nema raina ma. Ka zauna lafiya tare da ni.”
<- 1 Sama’ila 211 Sama’ila 23 ->