2 Sai ya zaɓi sojoji dubu uku daga jama’ar Isra’ila. Ya keɓe dubu biyu su kasance tare da shi a Mikmash da kuma a tuddan yankin Betel. Ya kuma bar dubu ɗaya tare da ɗansa Yonatan a Gibeya a yankin zuriyar Benyamin. Sauran sojojin kuwa Shawulu ya sallame su su koma gidajensu.
3 Yonatan ya kai wa Filistiyawa hari a Geba, sai Filistiyawa suka sami labarin. Sai Shawulu ya sa aka busa ƙaho ko’ina a ƙasar ya ce, “Bari Ibraniyawa su ji!” 4 Haka kuwa dukan Isra’ila suka ji labari cewa, “Shawulu ya kai hari a ƙasar Filistiyawa, yanzu Isra’ila ta zama abin ƙi ga Filistiyawa.” Aka kira mutane su haɗu da Shawulu a Gilgal.
5 Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra’ilawa. Suka fito da kekunan-dawakan yaƙi dubu talatin, da masu hawan dawakai dubu shida, da sojoji masu yawa kamar yashi a bakin teku. Suka tafi Mikmash a gabashin Bet-Awen, suka kafa sansani a can. 6 Sa’ad da Filistiyawa suka fāɗa wa Isra’ilawa da yaƙi mai tsanani, suka sa su cikin wani hali mai wuya, sai Isra’ilawa suka ɓuya a kogwanni, da ciyayi, da duwatsu, da ramummuka, da rijiyoyi. 7 Waɗansunsu ma suka haye Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad.
11 Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?”
13 Sama’ila ya ce, “Ka yi wauta da ba ka bi umarnin da Ubangiji Allahnka ya ba ka ba. Da ka yi haka da Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra’ila har abada. 14 Amma yanzu, masarautarka ba za tă dawwama ba, Ubangiji ya riga ya sami wani wanda zuciyarsa ke ƙauna, ya naɗa shi shugaban mutanensa gama ba ka bi umarnin Ubangiji ba.”
15 Sama’ila ya tashi daga Gilgal ya tafi Gibeya a ƙasar Benyamin. Shawulu kuma ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, yawansu ya kai wajen mutum ɗari shida.
19 Ba a sami maƙeri ɗaya a dukan ƙasar Isra’ila ba domin Filistiyawa sun ce, “In ba haka ba Ibraniyawa za su ƙera wa kansu takuba ko māsu.” 20 Saboda haka dukan Isra’ila sukan gangara zuwa wajen Filistiyawa domin su gyara bakin garemaninsu, da fartanansu, da gaturansu, da kuma laujunansu. 21 Duk lokacin da za su gyara bakin garmansu da fartanyarsu sai sun biya tsabar azurfa[a] biyu. Haka ma idan za su gyara gatari ko bakunan abin korar shanun noma sai sun biya tsabar azurfa ɗaya.
22 A ranar da yaƙi ya tashi, ba a sami wanda yake da takobi ko māshi ba a cikin mutanen da suke tare da Shawulu da Yonatan. Sai dai Shawulu da ɗansa Yonatan kaɗai.
- a tsabar azurfa. Da Ibraniyanci an rubuta biyu bisa uku na Shekel ne a nan. A zamaninsu wannan kuɗi ne mai yawa.