1 Sa’ad da Hiram sarkin Taya ya ji an shafe Solomon sarki yă gāji mahaifinsa Dawuda, sai ya aika da jakadunsa zuwa wurin Solomon, gama shi da Dawuda abokai ne sosai dukan kwanakinsa. 2 Solomon ya mayar da wannan saƙo ga Hiram ya ce,
7 Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.”
8 Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan,
10 A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata. 11 Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara. 12 Ubangiji ya ba wa Solomon hikima, kamar yadda ya yi masa alkawari. Dangantakar zaman lafiya ta kasance tsakanin Hiram da Solomon, su biyun suka yi yarjejjeniya.
13 Sarki Solomon ya ɗebi ma’aikata daga dukan Isra’ila, su dubu talatin. 14 Ya riƙa aika su dubu goma-goma zuwa Lebanon kowane wata, saboda su yi wata ɗaya a Lebanon, watanni biyu kuma a gida. Adoniram ne ya lura da aikin gandun. 15 Solomon ya kasance da ’yan ɗauko guda dubu saba’in da masu yankan duwatsu guda dubu tamanin a cikin tuddai, 16 ya kuma kasance da shugabanni dubu uku da ɗari uku waɗanda suke lura da aikin, su ne kuma suke bi da ma’aikatan. 17 Bisa ga umarnin sarki sai suka cire manyan duwatsu masu kyau don a tanada tushen duwatsun da aka gyara domin haikalin daga wurin haƙar duwatsun. 18 Gwanayen Solomon da na Hiram da kuma mutanen Gebal[a], su suka yanka, suka kuma shirya katako da dutse don ginin haikali.
<- 1 Sarakuna 41 Sarakuna 6 ->- a Wato, Baibilos.