Link to home pageLanguagesLink to all Bible versions on this site
19
Iliya ya gudu zuwa Horeb
1 Ahab fa ya faɗa wa Yezebel kome da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe dukan annabawan da takobi. 2 Saboda haka Yezebel ta aika da ɗan aika wa Iliya yă faɗa masa, “Bari alloli su hukunta ni da tsanani, in war haka gobe ban mai da ranka kamar na ɗaya daga cikin annabawan Ba’al ba.”

3 Iliya ya ji tsoro, ya gudu don yă ceci ransa. Sa’ad da ya kai Beyersheba a Yahuda, sai ya bar bawansa a can. 4 Shi kuma ya yi tafiya yini guda zuwa cikin hamada. Ya zo wurin wani itacen tsintsiya, ya zauna a ƙarƙashinsa, ya roƙa yă mutu. Ya ce, “Ya ishe ni haka, Ubangiji, ka ɗauki raina; ban fi kakannina ba.” 5 Sa’an nan ya kwanta a ƙarƙashin itacen ya yi barci.

Farat ɗaya sai wani mala’ika ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci.” 6 Ya duba kewaye, sai ga wainar burodi kusa da kansa a bisa garwashin wuta mai zafi, da kuma tulun ruwa. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya sāke kwanta.

7 Mala’ikan Ubangiji ya sāke dawowa sau na biyu ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci, gama tafiyar za tă yi maka yawa.” 8 Saboda haka ya tashi ya ci, ya kuma sha. Ta wurin ƙarfin da ya samu saboda wannan abinci, ya yi tafiya yini arba’in da dare arba’in, sai da ya kai Horeb, dutsen Allah. 9 A can ya shiga kogo ya kwana.

Ubangiji ya bayyana wa Iliya
Sai maganar Ubangiji ta zo masa, ta ce, “Me kake yi a nan, Iliya?”

10 Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.”

11 Sai Ubangiji ya ce, “Fita ka tsaya a kan dutse a gaban Ubangiji, gama Ubangiji yana shirin wucewa.”

Sai ga babbar iska mai ƙarfi ta tsage duwatsu, ta kuma ragargaza duwatsu a gaban Ubangiji, amma Ubangiji ba ya cikin iskar. Bayan iskar sai aka yi girgizar ƙasa, amma Ubangiji ba ya cikin girgizar ƙasa. 12 Bayan girgizar ƙasa, sai ga wuta, amma Ubangiji ba ya cikin wuta. Bayan wutar kuma sai ga wata ’yar murya. 13 Sa’ad da Iliya ya ji ta, ya ja mayafinsa ya rufe fuskarsa, ya fita ya tsaya a bakin kogon.
Sai ya ji murya ta ce masa, “Me kake yi a nan, Iliya?”

14 Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.”

15 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ka koma ta hanyar da ka zo, ka tafi Hamadan Damaskus. Sa’ad da ka kai can, ka shafe Hazayel yă zama sarki bisa Aram. 16 Ka kuma shafe Yehu ɗan Nimshi yă zama sarkin Isra’ila, ka shafe Elisha ɗan Shafat daga Abel-Mehola yă gāje ka a matsayin annabi. 17 Yehu zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Hazayel, Elisha kuwa zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Yehu. 18 Duk da haka zan bar mutane dubu bakwai na Isra’ila waɗanda ba su rusuna da gwiwansu wa Ba’al ba, ba su kuma sumbace shi da bakinsu ba.”

Kiran Elisha
19 Sai Iliya ya tafi daga can ya sami Elisha ɗan Shafat, yana noma da shanu goma sha biyu masu garman noma, shi kansa yana jan na goma sha biyun. Iliya ya tafi wurinsa ya jefa mayafinsa a kan Elisha. 20 Sai Elisha ya bar shanun, ya ruga ya bi Iliya. Ya ce, “Bari in sumbace mahaifina da mahaifiyata, in yi musu bankwana, sa’an nan in zo in bi ka.”
Iliya ya ce, “Koma! Me na yi maka?”

21 Sai Elisha ya bar shi, ya koma, ya ɗauki shanunsa ya yayyanka. Ya ƙone kayan garman noman don yă dafa naman, ya kuma ba wa mutane naman, suka kuwa ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya kuma zama mai hidimarsa.

<- 1 Sarakuna 181 Sarakuna 20 ->