1 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Yehu ɗan Hanani game da Ba’asha, 2 “Na ɗaga ka daga ƙura na mai da kai shugaban mutanena Isra’ila, amma ka yi tafiya a hanyoyin Yerobowam, ka kuma sa mutanena Isra’ila suka yi zunubi, ka tsokane ni na yi fushi ta wurin zunubansu. 3 Saboda haka ina gab da cinye Ba’asha da gidansa, zan kuma mai da gidanka kamar na Yerobowam ɗan Nebat. 4 Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ba’asha da suka mutu a birni, tsuntsaye kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.”
5 Game da sauran ayyukan mulkin Ba’asha, abin da ya yi, da kuma nasarorinsa, an rubuta su cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. 6 Ba’asha ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Tirza. Sai Ela ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
7 Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam.
9 Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza. 10 Zimri ya shiga, ya buge shi ya kashe a shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda. Sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki.
11 Nan da nan sai ya fara mulki ya kuwa zauna a kujerar sarauta, ya kashe dukan iyalin Ba’asha. Bai bar namiji guda ɗaya ba, ko dangi, ko aboki. 12 Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu. 13 Wannan ya faru saboda dukan zunuban Ba’asha da waɗanda ɗansa Ela ya yi, da ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani.
14 Game da sauran ayyukan mulkin Ela, da dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
20 Game da sauran ayyukan mulkin Zimri, da tawayen da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
23 A shekara ta talatin da ɗaya na Asa sarkin Yahuda, Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu, shekaru shida a Tirza. 24 Ya saya tudun Samariya daga Shemer, a bakin talentin biyu na azurfa, ya kuma gina birni a kan tudun, ya kira shi Samariya, bayan Shemer, sunan mai tudun a dā.
25 Amma Omri ya yi mugunta a gaban Ubangiji, ya kuma yi zunubi fiye da dukan waɗanda suka kasance kafin shi. 26 Ya yi tafiya a dukan hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat da kuma cikin zunubinsa wanda ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani.
27 Game da sauran ayyukan mulkin Omri, abin da ya yi, da kuma abubuwan da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila. 28 Omri ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Samariya. Sai Ahab ya gāje shi a matsayin sarki.
34 A lokaci Ahab ne, Hiyel mutumin Betel ya sāke gina Yeriko. Ya kafa tushensa a bakin ran ɗan farinsa Abiram, ya kuma kafa ƙofofinsa a bakin ran autansa Segub, bisa ga maganar Ubangiji da ya yi ta wurin Yoshuwa ɗan Nun.
<- 1 Sarakuna 151 Sarakuna 17 ->