3 Gama abu farko mafi muhimmancin da na karɓo shi ne na ba ku cewa Kiristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga Nassi, 4 cewa an binne shi an kuma tashe shi a rana ta uku bisa ga Nassi, 5 cewa ya bayyana ga Bitrus, sa’an nan ga Sha Biyun. 6 Bayan haka, ya bayyana ga fiye da ɗari biyar daga cikin ’yan’uwa a lokaci guda. Yawancinsu kuwa suna nan da rai, ko da yake waɗansu sun riga sun yi barci. 7 Sa’an nan ya bayyana ga Yaƙub, sa’an nan ga dukan manzannin, 8 a ƙarshe duka, ya bayyana a gare ni, kamar wanda an haifa a lokacin da bai kamata ba.
9 Gama ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzanni, ban kuma isa a kira ni manzo ba, domin na tsananta wa ikkilisiyar Allah. 10 Amma bisa ga alherin Allah, na zama abin da nake, alherinsa zuwa gare ni kuwa bai zama a banza ba. A’a, na yi aiki fiye da dukansu, duk da haka, ba ni ba ne, sai dai alherin Allah da yake tare da ni ne. 11 To, ko ni ne, ko su ne, wannan shi ne abin da muke wa’azi, shi ne kuma abin da kuka gaskata.
20 Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci. 21 Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum. 22 Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi. 23 Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa. 24 Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko. 25 Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa. 26 Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa. 27 Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.”[a] To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi. 28 Sa’ad da ya yi haka, sa’an nan Ɗan kansa yă koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yă zama kome da kome.
29 To, in babu tashin matattu, mene ne waɗanda ake musu baftisma saboda matattu za su yi? In ba a tā da matattu sam, me ya sa ake yin wa mutane baftisma saboda su? 30 Mu ma don me muke sa kanmu cikin hatsari a kowace sa’a? 31 Ina fuskantar mutuwa kowace rana. I, kamar yadda yake tabbatacce cewa ina taƙama da ku cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu. 32 In na yi kokawa da mugayen namomin jeji a Afisa bisa ga ra’ayin mutane ne kawai, mece ce ribata, in har ba a tā da matattu? Ai,
42 Haka ne tashin matattu zai kasance. Abin da aka shuka yakan ruɓe, abin da aka tā da shi kuma ba ya ruɓewa; 43 akan shuka shi cikin ƙasƙanci, a kuma tā da shi cikin ɗaukaka, akan shuka shi da rashin ƙarfi, a kuma tā da shi da ƙarfi; 44 akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma tā da shi da jikin ruhaniya.
50 Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba. 51 Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu 52 farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu. 53 Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. 54 Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.”[d]
58 Saboda haka, ƙaunatattu ’yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu yă jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
<- 1 Korintiyawa 141 Korintiyawa 16 ->