7 Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba,[b] da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne. 8 Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji. 9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji. 10 Don haka, saboda wannan, da kuma saboda mala’iku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta. 11 Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba. 12 Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.
13 Ku kanku duba mana. Ya yi kyau mace tă yi addu’a ga Allah da kanta a buɗe? 14 Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi, 15 amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne. 16 In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata al’ada, haka ma ikkilisiyoyin Allah.
27 Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan. 28 Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin. 29 Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne. 30 Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci. 31 Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba. 32 Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.
33 Saboda haka ’yan’uwana, sa’ad da kuka taru don ci, ku jira juna. 34 In wani yana jin yunwa, sai yă ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yă jawo hukunci.
- a Ko kuwa al’adu
- b Ko kuwa 4 Duk namijin da ya yi addu’a ko annabci da dogon gashin kai, ya rena kansa. 5 Duk macen da ta yi addu’a ko annabci ba tare da ta rufe gashin kanta ba kuwa ta rena kanta, ta yi kama da ɗaya a cikin “matan da aka yi wa aski.” 6 In mace ba ta da abin rufuwa, sai tă kasance mai aski kwal a kanta, amma da yake abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske kanta, ya kamata tă sa yă yi girma kuma. 7 Bai kamata namiji yă kasance da dogon gashin kai ba