3 Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa.
16 Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa ’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna.
17 Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berekiya daga cikin ’yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kushahiya. 18 Tare da su kuma ’yan’uwansa da suke biye bisa ga matsayi. Wato, Zakariya,[a] Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ben, Ma’asehiya, Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom da Yehiyel,[b] matsaran ƙofofi.
19 Mawaƙan nan Heman, Asaf da Etan, ne za su buga kugen tagulla. 20 Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot. 21 Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom, Yehiyel da Azaziya, ne za su ja garayu masu murya ƙasa-ƙasa bisa ga sheminit. 22 Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni.
23 Berekiya da Elkana, ne za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin. 24 Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.
25 Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-Edom, da farin ciki. 26 Domin Allah ya taimaki Lawiyawan da suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, aka miƙa hadayar bijimai bakwai da raguna bakwai. 27 To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin. 28 Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.
29 Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal ’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta.
<- 1 Tarihi 141 Tarihi 16 ->